Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a Abuja ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar Nasarawa, inda ta mayar wa Gwamna Abdullahi Sule nasara kamar yadda hukumar INEC ta bayyana a lokacin zaɓen gwamnan jihar na 2023.
Alfijir Labarai ta rawaito hukuncin da kotun ta yanke yau Alhamis, alƙalan kotun sun bayyana cewa kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamnan jihar Nasarawa ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke.
A watan da ya gabata ne dai kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar Nassarawa ta soke nasarar gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC, tare da bayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris ɗin 2023.
Tun farko, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, a sakamakon zaɓen gwamnan jihar ta ce Abdullahi Sule na APC ya samu ƙuri’a 347,209, inda ta ce ya doke Ombugadu na PDP, wanda ya samu ƙuri’a 283,016.
Sai dai rashin gamsuwa da hakan ne ya sa jam’iyyar PDP da ɗan takararta suka garzaya kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamna, wanda a ranar 2 ga watan Oktoba ta soke nasarar ta gwamna Sule.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
Hakan ne ya sanya APC da lauyoyinta suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun ɗauka ƙara da ke Abuja wadda ke zaman yanke hukuncin a yau Alhamsi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp