Da Ɗumi Ɗuminsa! IPMAN Ta Janye Umarnin Yajin Aiki

Alfijr ta rawaito Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta janye umarnin dakatar da ayyuka tare da umurtar mambobinta a fadin kasar da su yi watsi da umarnin da aka bayar a baya.

Shugaban IPMAN na kasa, Dattijo Chinedu Okoronkwo ne ya bayar da wannan umarni ta hannun shugaban kungiyar IPMAN shiyyar Kano, Alhaji Bashir Dan Malam a ranar Talata.

Ya ce umarnin ya biyo bayan taron da aka yi tsakanin mahukuntan hukumar ta NNPC, IPMAN na kasa da masu ruwa da tsaki inda hukumar ta NNPC ta yi alkawarin baiwa ‘yan kasuwa man fetur kai tsaye.

Danmalam ya ce taron wanda ya gudana a misalin hukumar ta NNPC, an yi shi ne domin lalubo hanyoyin magance matsalar karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan.

Idan ba a manta ba a baya shugaban kungiyar ta IPMAN a jihar Borno, Mohammed Kuluwu ya umurci mambobin kungiyar da su dakatar da duk wasu ayyuka baya ga dakatar da biyan kudaden da ake ba da odar kayayyakin daga tushe har sai an sanar da su.

Danmalam ya ce dalilin da ya sa Kuluwu ya ba da wannan umarni shi ne saboda su a Kasuwa sun sayi kayayyakin da tsada sosai saboda ba sa samun kayayyakin daga Depots masu zaman kansu.

“Bayan ganawar, hukumar NNPCPL ta yi alkawarin baiwa IPMAN kayayyakin kai tsaye, sannan kuma ta umurci direbobin tankar man fetur da su dakatar da karbar harajin N2,” in ji Danmalam

Ya kuma jaddada aniyar kungiyar na ci gaba da jigilar kayayyakin zuwa dukkan jihohin kasar nan domin kawo karshen karancin kayayyakin da ake fama da su.

Ya ce Okoronkwo ya yi amfani da wannan dama wajen gargadin ‘yan kungiyar da kada su bari ‘yan siyasa su yi amfani da su domin cimma muradun su na son kai.

“Ina so in yi kira ga mambobinmu da kada su bari ‘yan siyasa su yi amfani da su don son rai, musamman a yanzu da zabe ya gabato.” Inji Danmalam.

A cewarsa, IPMAN za ta ci gaba da tallafawa Gwamnatin Tarayya don tabbatar da samar da mai ba tare da katsewa ba a lunguna da sako na kasar nan.

Shugaban IPMAN na kasa ya kuma yabawa Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya Limited karkashin jagorancin Mele Kyari bisa jajircewarsa na kawo karshen matsalar man fetur da ake fama da ita a kasar nan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *