Da Ɗumi Ɗuminsa: Hukumar WAEC ta nada sabon shugaba a Najeriya

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta Yamma (WAEC) ta nada Dr. Amos Josiah Dangut a matsayin shugaba a Najeriya.

Dr. Dangut ya maye gurbin Patrick Areghan, wanda wa’adinsa zai kare a wannan watan.

A cewar sanarwar da WAEC ta fitar a ranar Litinin, Dangut ya taba rike mukamin mataimakin magatakarda/HNO.

Sanarwar ta bayyana cewa ya shiga aikin WAEC ne a shekarar 1998 a matsayin mataimakin magatakarda na biyu kuma ya haye matsayi har ya zama mataimakin magatakarda a watan Afrilun 2018.

Ya lashe lambar yabon Kwamitin Jarrabawar Najeriya kan gudanar da jarrabawar tsakanin 2000 zuwa 2006.

“Ya yi aiki a matsayin Mataimakin Magatakarda/Subject Officer, Sashen Bunkasa Jarabawa, WAEC, Legas (Yuli 1998 – Janairu 2005);

Ya sake zama babban Mataimakin Magatakarda/Shugaban Tsaro na Jarrabawa da Mataimakin Shugaban Reshe, Ofishin Reshen Uyo (Janairu 2005 – Janairu 2008);

Hakazalika ya jike babban Mataimakin Magatakarda/Shugaban Tsaro na Jarrabawa da Mataimakin Shugaban Reshe, Ofishin Reshen Bauchi (Janairu 2008 – Disamba 2011);

Sai ya zama babban mataimakin Magatakarda/Mai Kula da Reshe, Ofishin Reshen Yola (Disamba 2011 – Janairu 2019);

Sai kuma mataimakin magatakarda/Mai kula, Sashen Jarabawa Bayan (Janairu 2019 – Oktoba, 2020); Mataimakin magatakarda / mai kula da shiyyar, ofishin shiyya na Ikeja.

“An haifi Dangut ne a ranar 2 ga Oktoba, 1967, a gundumar Mbar da ke karamar hukumar Bokkos, a Jihar Filato.

Ya halarci Makarantar Sakandare ta Gwamnati, Riyom (1981 zuwa 1983) da Makarantar Kimiyya ta Gwamnati, Kuru (1983 zuwa 1986), inda ya samu WASC/SC a 1986, duka a Jihar Filato;

Daga nan ya wuce Jami’ar Aikin Gona ta Makurdi ta Jihar Binuwai, inda ya samu lambar yabo ta digirin digirgir a fannin noma a shekarar 1991.”

Sanarwar ta kara da cewa, “A cikin shekaru 25 da suka gabata, ya yi amfani da fasahar Watsa Labarai da Sadarwa don inganta sabbin hanyoyin inganta gwaji, gudanar da Gwaji, da ayyukan Gwaji.

“Dangut hazikin malami ne da ke da wallafe-wallafe daban-daban na ilimi a cikin mujallu na duniya da na kasa.

Ya kuma gabatar da makalu da dama da sauran kasidu a taron duniya da na kasa baki daya. “

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *