Da Ɗumi Ɗuminsa! CBN Ya Umurci Bankuna Su Ci Gaba Da Karɓar Tsofaffin 1,000 da 500

Alfijr ta rawaito  Bankin CBN ya umurci bankunan kasar su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin naira 1,000 da 500 waɗanda yawansu bai zarta N500,000 ba.

Bankin na CBN ya bayyana haka ne a yau Juma’a, bayan koke-koken da ake ta samu a faɗin ƙasar kan wahalar da al’umma ke fuskanta wajen samun sababbin kuɗin.

Mai magana da yawun babban bankin, Osita Nwanisobi ya tabbatar wa BBC da wannan bayani.

Karin Bayani na nan tafe…

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *