Da Ɗumi Ɗuminsa! Majalisar Wakilai Tayi Sammacin Gwamnan Bankin CBN

Daga

Aminu Bala Madobi

Alfijr ta rawaito Majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeriya da ya dakatar da shirin aiwatar da sabuwar manufar cire kudaden da aka shirya kaddamar wa ranar 9 ga watan Junairu, 2023 har sai an cika sharuddan dokar da ta kafa bankin.

Hakazalika majalisar ta kuma gayyaci gwamnan babban bankin Godwin Emefiele kamar yadda dokar babban bankin kasar ta tanada domin ya yiwa majalisar bayani kan manufofin bankin.

Zauren majalisar ya fusata a ranar Alhamis yayin da ‘yan majalisar ke yin Allah wadai da sabuwar manufar cire kudaden, suna masu cewa hakan zai yi matukar shafar kananan ‘yan kasuwa da tattalin arziki tunda akasarin al’ummomin karkara ba su da damar hada hada banki.

Sai dai kuma bayan wani batu da Mark Gbillah ya gabatar, Majalisar ta umurci Gwamnan CBN da ya gurfana gaban majalisar a ranar Alhamis 15 ga watan Disamba, 2022 domin yi wa majalisar bayani kan dalilin da ya sa ya dage kan takaita cirar adadin kudaden.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

2 Replies to “Da Ɗumi Ɗuminsa! Majalisar Wakilai Tayi Sammacin Gwamnan Bankin CBN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *