Da Ɗumi-Ɗuminsa: Kotu ta umarci INEC ta soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu

IMG 144617 15626 1781531190852

Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyun siyasa biyar da suka haɗa da ADC, Accord Party, Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA) da Zenith Labour Party (ZLP).

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin bayan ƙungiyar tsoffin ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa ta kai ƙara tana neman kotu ta tabbatar da cewa INEC na da nauyin doka na cire duk wata jam’iyya da ta gaza cika sharuddan da kundin tsarin mulki ya gindaya domin ci gaba da kasancewa a matsayin jam’iyya mai rajista.

Masu ƙarar sun bayyana cewa jam’iyyun biyar sun kasa samun sakamakon da doka ta tanada a zaɓukan 2023 da kuma zaɓukan cike gurbi, inda ba su samu kujerun zaɓe a matakan tarayya, jihohi ko ƙananan hukumomi ba.

Kotun ta amince da hujjar cewa ci gaba da barin waɗannan jam’iyyu a cikin tsarin siyasa ya saɓa wa tanade-tanaden doka, tare da umartar INEC ta soke rajistarsu kafin shirye-shiryen zaɓen 2027 su ƙara nisa.

Rahotanni sun nuna cewa hukuncin na iya shafar damar wasu ‘yan takara, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, idan har suka yi niyyar tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyun da abin ya shafa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.: Kotu ta umarci INEC ta soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu

Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyun siyasa biyar da suka haɗa da ADC, Accord Party, Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA) da Zenith Labour Party (ZLP).

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin bayan ƙungiyar tsoffin ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa ta kai ƙara tana neman kotu ta tabbatar da cewa INEC na da nauyin doka na cire duk wata jam’iyya da ta gaza cika sharuddan da kundin tsarin mulki ya gindaya domin ci gaba da kasancewa a matsayin jam’iyya mai rajista.

Masu ƙarar sun bayyana cewa jam’iyyun biyar sun kasa samun sakamakon da doka ta tanada a zaɓukan 2023 da kuma zaɓukan cike gurbi, inda ba su samu kujerun zaɓe a matakan tarayya, jihohi ko ƙananan hukumomi ba.

Kotun ta amince da hujjar cewa ci gaba da barin waɗannan jam’iyyu a cikin tsarin siyasa ya saɓa wa tanade-tanaden doka, tare da umartar INEC ta soke rajistarsu kafin shirye-shiryen zaɓen 2027 su ƙara nisa.

Rahotanni sun nuna cewa hukuncin na iya shafar damar wasu ‘yan takara, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, idan har suka yi niyyar tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyun da abin ya shafa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *