Alfijr ta rawaito Bankin CBN da bankin NIRSAL sun soma kwato bashin da suka bawa mutane rance ta hanyar dibar kudin kai tsaye a asusun ajiyar mutane.
Alfijr Labarai
Idan zaku tuna a kwanakin baya bankin ya fitar da sanarwa kan maganar duk wanda ya san ya karbi bashin yayi kokarin biya idan kuma bai biya ba zasu karbi kudadensu tare da haɗin guiwa da hukumar EFCC.
A ranar Juma’a da ta gabata ne mutane da yawa wadanda suka karbi bashin suka soma samun sakon kar ta kwana, na kwasar kudi daga asusun ajiyarsu na banki,
Mutane da dama sun sami kansu cikin wannan halin na zabtare musu kudade a asusunsu, Sakamakon kunnen ƙashi da suka yi ko kuma shakulatin bangaro kan biyan kuɗin.
Alfijr Labarai
Sanarwar da bankin ya fitar yace, waɗanda suka ci gajiyar bashin bankin NIRSAL karkashin tsarin COVID-19 da ‘AGSMEIS’ da kuma ‘Anchor Borrowers Programme’ su abin yake shafa.
Daraktan kuɗi na bankin CBN Mista Philip Yila ya bayyana cewar, duk wanda ya ci bashin mu sai ya biya, domin muna da BVN din kowa, kuma za mu yi amfani da tsarin GSI don karbo kudaden mu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb
Very nice