CBN ya magantu akan kin karbar tsofaffin takardun Naira a kasar

CBN Governor

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gargaɗi masu ƙin karɓar tsofaffin takardun Naira a faɗin ƙasar.

Alfijir Labarai ta rawaito wannan na zuwa ne sakamakon fargabar da ake ciki cewa tsofaffin takardun kuɗi za su daina aiki nan da watan Disamba 2023.

Wata sanarwar da mai magana da yawun bankin CBN, Isah Abdulmunin ya fitar a ranar Laraba, ta ce bankin bai bayar da umarnin janye tsofaffin takardun kuɗi ba daga wajen al’umma.

Bankin ya ce, “An kuma samu rahotannin damuwa da wasu jama’a ke nunawa kan halacci ko rashinsa na tsoffin takardun kuɗin Naira.

“Don kauce wa shakku, yayin da muke nanata cewa akwai isassun takardun kudi a faɗin ƙasar nan don gudanar da duk harkokin tattalin arziki na yau da kullun, muna so kuma mu bayyana cewa duk wata takardar kuɗi da Babban Bankin Najeriya, za ta ci gaba da aiki kuma bai kamata a yi watsi da ita ba, kamar yadda yake a sashe na 20(5) na dokar CBN, na 2007.

Babban bankin ya umarci rassansa a faɗin ƙasa da su ci gaba da bayar da tsofaffin takardun kuɗi da kuma sabbi don ci gaba da rarrabawa ga abokan hulɗar bankuna.

CBN
CBN Press release

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *