Buhari ya tura tawagar jami’an tsaro ta musamman zuwa Sokoto da Katsina don dakile ayyukan ’yan bindiga

Shugaba Muhammadu Buhari ya tura  tawagar jami’an tsaro ta musamman zuwa jihohin Sokoto da Katsina don dakile ayyukan ’yan bindiga a jihohin.

Best Seller Channel 

 Malam Garba Shehu ne, ya sanar da hakan a ranar Juma’a, ya ce Buhari na jiran rahoto cikin gaggawa da kuma shawarwari kan matakin da ya kamata a dauka domin magance matsalolin da jihohin ke fuskanta.

Tawagar da aka aka tura ta hada da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da Shugaban Sashen Kwararru na Tsaron Kasa, Manjo-Janar Samuel Adebayo da kuma Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba.

Best Seller Channel 

Sauran sun hada da Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, Yusuf Magaji Bichi, da Darakta-Janar na Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Najeriya Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewar wannan matakin dai na zuwa ne bayan mutane daga yankin Arewacin kasar sun nuna bacin ransu kan kasshe-kashen da ake musu tare da garkuwa da mutane a yankin.

Jama ar Arewacin Nigeria a yau Juma a suka fito suka gudanar da zanga-zangar neman Shugaba Buhari ya sauka daga mulki saboda gazawarsa wajen kare rayuka da yayi alkawarin karewa.