Budurwa Tayi Sanadin Ɗalibi Ya Kashe Abokin Karatunsa Da Wuƙa A Bauchi

Alfijr ta ruwaito, lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba, 2022 da misalin karfe 11 na safe a daya daga cikin gidajen mai suna MD Burra dake kan titin Lagos, biyo bayan wata hatsaniya kan wanene saurayin wata daliba tsakanin abokai

Marigayi Usman har zuwa rasuwarsa dalibin Biochemistry ne wanda zai kamala ranar Juma’a 9 ga watan Disamba 2022 lokacin da ake sa ran zai rubuta takardar karshe na karatunsa.

Wani shaidar gani da ido da daya daga cikin Daliban da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, “A ranar kaddara, an yi ta cece-kuce tsakanin abokanan biyu a kan wanene ainihin saurayin wata daliba kamar yadda su biyun ke zarginta”.

Ya kara da cewa “Marigayi Usman ya ce ya bar masa yarinyar (Kamal) wanda ya yi gargadin cewa kada a sake ganinsa a kusa da yarinyar ko kuma ya zargi kansa kan duk abin da ya same shi, shi ya jiyo.

Daga nan sai muka ce wa Usman ya bar yankin domin gujewa duk wata matsala”.

“Usman ya koma daki ya dauki kayansa, yana shirin fita, duk muna tsaye sai ga Kamal ya bishi da gudu, bamu san yana rike da wuka a hannunsa ba, sai ya ruga da gudu, ya caka masa wuka a gefe sau uku.

Sai Usman ya fadi kasa da jini yana ta kuwwa,” in ji shi.

Shaidan ya kara da cewa daliban da ke kusa da su sun hada kai suka kai shi asibitin makarantar.

“Mun san cewa ya mutu a wannan lokacin amma domin gudun tashin hankalin da daliban ke yi, sai mahukuntan makarantar suka ce sun garzaya da shi asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa don ci gaba da kula da shi.”

Ya kuma ce “Da jin labarin ne dalibai suka kama Kamal suka fara dukansa kafin jami’an tsaron makarantar su kubutar da shi.

Yana takama da cewa mahaifinsa Sajan Dan Sanda ne kuma babu abin da zai same shi”in ji shaidar.

A cewarsa, “A matsayinmu na jami’an SUG, muna jiran mu ga abin da zai faru, idan muka lura da wani wasa da aka yi da ba daidai ba, za mu dauki namu matakin.

Mun san Kamal mai shaye shaye ne alhalin marigayi Usman yana shan taba, hasali ma Kamal ya sha a daren jiya kafin faruwar lamarin”.

Sai dai ya jaddada cewa sun kasance abokan juna kafin faruwar lamarin, kuma babu wata matsala da aka samu a tsakanin su kafin ranar da lamarin ya faru, yayin da ya yi kira ga mahukuntan makarantar da su tabbatar an yi adalci wajen ganin an shawo kan iyalan marigayi Usman.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *