Biyo Bayan Zaluntar Wani N3m, Rundunar yan Sandan Nijeriya Ta Tube Kakin Jami’an Ta 5

FB IMG 1720009838906

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta tube wa wasu jami’an ta biyar kaki sakamakon zargin su da karbar cin hancin kudi kimanin Naira milyan uku

Alfijir labarai ta ruwaito mataimakin Shugaban ’Yan Sanda mai kula da Shiyya ta shida da ke Jihar Kuros Riba, Jonathan Towuru, ya sanar cewa ’yan sandan sun kwace kudin ne da bakin bindiga a hannun wani mai abin hawa a jihar Kalaba.

A makon jiya ne aka zargi jami’an da kwatar kudin da bakin bindiga a hannun wani mutum da rundunar ta sakaya sunansa.

Yanzu haka wadanda ake zargin an tube masu kaki amma ana tsare da su ana bincike, da zarar an same su da laifi kotu za a turasu ta yanke masu hukuncin da ya dace.

Ko a kwanan baya irin haka ta taba faruwa a kan babbar hanyar Kalaba zuwa Ikom inda aka kama wasu ’yan sanda kan karbar na goro.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *