Bikin Sallah Lokacine Da Musulmai Ke Kara Nunawa Juna kauna Da Yafiya – Yalleman

Alfijr ta rawaito Kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa reshen Freedom Radio ta taya alummar Musulmai Murnar Bikin Ƙaramar Sallah Ta Bana

Wannan sako na cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannu shugabar kungiyar Hajiya Aisha Muhammad Yalleman da Kuma sakataren kungiyar Muzammil Ibrahim Yakasai.

Yalleman ta ce, lokacin bikin karamar sallah lokacine da ya kamata musulmai su Kara nunawa juna kauna da sadakarwa da yafiya da Kara rubanya yin ayyuka don samun kusancin Allah madaukakim sarki, tare yiwa Kasa addur samun zaman lafiya.

Sanarwar ta Kuma bukaci ‘yan Jaridu da su ci gaba da gudanar ayyukansu bisa tsarin kundin kasa na ‘yan Jarida.

Hajiya Aisha ta Kuma yi kira ga Sabbin shugabanni da aka zaba da su Kara himma wajen warware matsalolin da Najeriya ke fuskanta, kama daga rashin tsaro da siyasa da Ilimi da lafiya da Kuma bangaren Noma.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *