BBC ta dakatar da wani babban ma’aikacinta da ke gabatar da shirye-shirye bayan da aka zarge shi da biyan wata matashiya mai ‘yan shekara 17, makudan kuɗaɗe domin ta tura masa hotunanta na batsa.
Alfijir Labarai ta rawaito cikin sanarwar dakatarwar da hukumar gudanarwar BBC ta fitar ta ce ”tana ɗaukar duk wani zargi da aka yi wa ma’aikatanta da matuƙa muhimmanci”.
”Wannan batu ne mai sarkakiya, kuma BBC tana yin duk abin da ya kamata domin gano hakikanin gaskiyar abin da ya faru domin ɗaukar matakin da ya dace”.
An kuma gano cewa BBC ta tuntuɓi rundunar ‘yan sanda a wani ɓangare na binciken nata.
Sakatariyar Al`adu da wasanni ta Birtaniya Lucy Frazer za ta yi ganawar gaggawa da Babban daraktan BBC a wannan yau Lahadi kan lamarin.
Cikin wata sanarwa ma`aikatar Al`adu da Yaɗa Labarai da Wasanni ta bayyana zarge-zargen a matsayin ‘abin damuwa ƙwarai’.
Zargin da Jaridar Sun ta fara wallafa ya bayyana yadda iyalan matashiyar su ka yi wa BBC ƙorafi tun cikin watan Mayu.
Sashen al`adun ya ce ya zama tilas BBC ta yi binciken ƙwaƙwaf, bayan Miss Frazer ta shirya don ganawar musamman da Tim Davie shugaban BBC.
Mahaifiyar matashiyar ta shaida wa Jaridar Sun a ranar Lahadi cewar an fara biyan kuɗaɗen ne tun yarinyar na da shekaru 17, Kuma matashiyar ta yi amfani da kuɗaɗen wajen ɗaukar nauyin wata ƙungiyar da ke yaƙi da hada-hadar hodar iblis.
‘Ta kuma ƙara da cewa idan aka ci gaba da biyan kuɗaɗen da ake zargi, ya cigaba ƴar ta mai shekaru 20 a yanzu za ta iya rasa ranta”.
Ta kuma yi ikirarin cewa an dauki hoton mai gabatar da shirye-shiryen sanye da gajeren wando yayin da yake magana da matashiyar a bidiyo .
Iyalan matashiyar sun ce bayan sun yi wa BBC ƙorafi sun cigaba da jin ma`aikacin yana gabatar da shirye-shirye, wannan ne dalilin da ya sa suka miƙa ƙorafinsu Jaridar Sun.
Jaridar Sun ta ce ta boye sunan ma`aikacin ne bisa dalilan shari`a
BBC ba ta sanar da sunan wanda ake zargin ba, amma ta sanar da cewar za a jima ba a ji muryarsa a Rediyo ba.
tun bayan bayyanar labarain masu gabatar da shirye-shirye na BBC suka fara wallafa sakonni a shafukansu na sada zumunta, inda suke bayyana cewa ba su ne wadanda ake zargi da aikata laifin ba.
Wakiliyar BBC Lucy Manning ta ce tun da farko an zargi Gidan Rediyon da rashin gudanar da bincike bayan iyalan matashiyar sun gabatar da ƙorafinsu.
Wasu Ƴan Siyasa sun ce akwai alamun lauje cikin naɗi a BBC, wadda ta jima tana ikirarin ɗaukar zarge-zarge da muhimmanci.
‘Yan siyasa sun buƙaci a dauki mataki
Victoria Atkins mamba a Jam`iyyar Conservative ta buƙaci a ɗauki mataki cikin gaggawa.
Yayin amsa tambayoyi cikin wani shirin BBC a ranar Lahadi Miss Reeves ta buƙaci BBC ta sanar da matakin da ta ɗauka kan wannan batu da kuma aiwatar da gyara.
Misis Atkins ta bayyana takaici game da zargin, wanda ta ce batu ne da ya shafi yarinya ƙarama wadda za ta shiga matsananciyar damuwa da fargaba don haka ta ja hankalin mutane su yi taka-tsan-tsan wajen tambayoyi da gudanar da rahotanni.
A lokacin shirin tattaunawar kai tsaye a BBC ƙwararren ɗan Jarida Stewart Purvis ya ce wannan tirka-tirka za ta ɓata sunan BBC musamman a matsayinta na kafar yaɗa labaran da ƙasa ta amince da ita.
Da aka tambaye shi wanne mataki zai ɗauka idan shi ma`aikacin BBC ne, sai ya ce shugabanni su tattaro waɗanda suka san abinda suke yi.
“Ku na buƙatar masu kula da ma`aikata, kuna buƙatar lauyoyi, kuna buƙatar waɗanda suka ƙware a magana, akwai kuma bukatar sanya ido kan shugabannin wanda ake zargin.”
“Ku sani duk saƙonnin email da kuka yi musaya a tsakaninku sai an bankaɗo shi. Aikin da ke kan shugabannin BBC ba ƙarami ba ne.”
Ranar Juma`a kakaki daga Ofishin Hulɗa da Jama`a na BBC ya ce: ” Mu na ɗaukar matakin da ya kamata kan duk wani zargi kuma mun yi tanadin yadda za mu fuskanci wannan al`amari.
A duk lokacin da muka samu bayanin da yake buƙatar zurfafa bincike, muna ɗaukar matakin da ya cancanta wanda ya haɗa da buƙatar yin magana da wanda ya tuntuɓe mu don gudanar da bincike.
Rashin samun martanin waɗanda suka tuntuɓe mu don ƙorafia, shi ne yake hana mu samun bayani gamsasshe don ɗaukar mataki.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ