Bayan Haihuwarsa Babu Dubura Yaron Ya Mutu Da Sanyin Safiyar Yau Lahadi

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Alfijr ta rawaito Jariri dan wata tara da haihuwa wanda aka haifa tare da laluran rashin lafiya a Saminaka Quarters, dake karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara ya rasu.

Mahaifin yaron Malam Ibrahim Lawali da ke zaune a saminaka quarters a karamar Hukumar Gusau , ya tabbatar da hakan ga manema labarai hakan a Gusau babban birnin jihar.

Idan za a iya tunawa yaron an haife shi ne ba dubura wanda hakan ya sa ya yi masa wahala wajen fitar da abin da ya ci, hakan ya sa iyayensa suka kai shi cibiyar kula da lafiya ta tarayya FMC Gusau domin neman magani, amma daga baya aka mayar da shi Usumanu Danfodio Teaching Hospital dake sokoto.

A cewarsa, an kashe naira dubu dari uku a UDUS domin yaron ya samu na’urar fitar da fitsari na wucin gadi inda zai fitar.

Ya kara da cewa, bayan gwaje-gwajen lafiya da bincike da aka yi a asibitin koyarwa na Usmanu Danfodio Sokoto, an yi hasashen naira dubu dari biyar za a yi wa yaron tiyata a karo na biyu domin samar da tsarin fitar da bayan gida.

Da yake magana kan lamarin a kwanakin baya Malam Lawali ya ce kudaden da ake nema na yi wa yaron tiyata na biyu da na uku ba a tara su ba ne don cika wa’adin da aka bayar kuma a karshe yaron ya rasu ne da sanyin safiyar yau Lahadi 12 ga Fabrairu, 2023.

Ya yaba da kokarin kungiyar NUJ Correspondents Chapel na jihar Zamfara na sanar da jama’a halin da lafiyar yaron ke ciki tare da bayar da gudunmawar kudi naira dubu hamsin a matsayin taimakonsu karkashin jagorancin Sani Haruna Dutsimma.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *