Bawa Ya Shiga Hannun DSS Bayan Dakatar Da Shi Daga Mukaminsa

Alfijir Labarai ta rawaito hukumar tsaro ta DSS a Nijeriya ta ce shugaban hukumar EFCC yana hannunta.

Wata sanarwa da DSS ta wallafa a shafinta na Twitter jim kadan bayan shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da AbdulRasheed Bawa daga kan mukaminsa, ta ce “ya iso” ofishinta “awanni kadan da suka gabata.”

Sanarwar da kakakin hukumar, Peter Afunanya ya sanya a hannu, ta kara da cewa an gayyaci AbdulRasheed Bawa don binciken da ake yi da ya shafe shi.

“Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da Mr. AbdulRasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar ta EFCC domin samun damar gudanar da binciken da ya dace kan ayyukan da ya yi lokacin da yake rike da ofishinsa,” in ji sanarwar

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *