An bayyana shugaban kwamitin majalisar dattawan Najeriya kan harkokin tsaro a yanzu, Sanata Shehu Buba a matsayin wanda ya dace ya gudanar da mulkin jihar Bauchi a zaben 2027. Wata kungiya a karkashin kungiya Mai suna Bauchi Transfomers Movements ce ta bayyana hakan.
Shugaban kungiyar Amb. Sani Muhammad Sani da Sakataren ta Bala Jibrin a wata ganawa da wasu zababbun manema labarai da suka gudanar a sakatariyar kungiyar na wucin gadi da ke Abuja sun bayyana cewa, Sanata Shehu Buba ya taka rawar gani a rayuwar talakawan jihar Bauchi na tsawon shekaru da dama.
“Tare da zuciyar zinare da sha’awar yin hidima, Sanata Buba ya sadaukar da rayuwar shi wajen karfafa rayuwar marasa galihu da al’ummomin da ke fama da talauci a fadin jihar.
“Sanata Buba, bisa namijin kokarin da yake yi, ya nuna jajircewar shi wajen kawo ci gaban al’umma. Jajircewar shi da sadaukar da kai ga ci gaban al’ummar shi ta jihar Bauchi , da kasa baki daya ya sa ya yi suna a matsayin gwarzo na gaskiya. Dan uwa na gaskiya kuma zakaran talakawa.”
Daya daga cikin manyan nasarorin da ya samu a cewar kungiyar ita ce goyon bayan da yake bayar wa masu karamin karfi.
Sanata Shehu Buba a cewar kungiyar ya ci gaba da yin amfani da matsayin shi da ya rike a matakai dabam-dabam wajen kara yada bukatun su da kuma neman masu maganin matsalolin su da bayar da tallafi ga al’ummomin da ke zaman kashe wando da kuma bayar da shawarwari ga masu karamin karfi.
Sanata Buba ya tabbatar da cewa shi abokin tarayyar jama’a ne na gaskiya ga masu bukata hidinar al’umma.
Kungiyar ta bayyana cewa Sanata Shehu Buba Yana amfanin da matsayin shi na shugaban kwamitin majalisar dattijawan Najeriya a kan harkokin tsaro wajen taka rawar gani gami da tabbatar da tsaro da zaman lafiyar al’ummar jihar Bauchi, Arewacin Najeriya da kuma kasa baki daya.
‘Yan kungiyar sun kara da cewa sanata Buba ya taka rawar gani wajen bunkasa da aiwatar da ingantaccen tsaro a matakan samar da tsaro da kwanciyar hankali ga ‘yan kasa.
“Gudunmawar sanata Buba ga ci gaban jihar Bauchi ba ta da iyaka. Ya kasance mai fafutukar kawo sauye-sauye masu yawa wadanda ke da nufin inganta rayuwa da jin dadin jama’a tun daga bangaren ilimi da kiwon lafiya zuwa karfafa tattalin arziki da ci gaban ababen more rayuwa.
“Yayin da yake ci gaba da yi wa al’ummar jihar Bauchi hidima, Sanata Shehu Buba ya ci gaba da jajircewa wajen ganin ya samar da kyakkyawar makoma ga kowa. Rashin son kai, tausayi da sadaukar da kai ga hidima ya sa ya zama jagora abin koyi.”
“Za mu ci gaba da fafutukar tabbatar da ya zama gwamnan a Jihar Bauchi a zabe mai zuwa na shekarar 2027.” inji Amb. Sani Muhammad Sani
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj