Bani Na Kar Zoman Ba A Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A NNPP – Shekarau

Alfijr ta rawaito Malam Ibrahim Shekarau ya ce shi da kansa ya rubuta wa INEC cewa a sauya sunansa saboda ya bar jam’iyyar, amma sai ta ce masa lokacin canza sunan ɗan takara ya wuce, sai dai, idan ɗan takara ne ya rasu, a wata tattaunawa da yayi da BBC

Ya ce tuni ya bar jam’iyyar NNPP kuma ba ita yake wakilta ba, inda ya ce ko da ya ci zaɓe ba a cikinta yake ba.

Sanata Shekarau ya kuma ce ya kira wanda yake takarar kujerar ta sanata a jam’iyyar NNPP, inda ya ce masa ya dakatar da yakin neman zaɓe saboda ba sunan shi ne a jerin sunayen da hukumar zaɓe ta san da su ba.

Ga alama an shiga ruɗani game da takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP kasancewar bayanai na nuna cewar har yanzu sunan Sanatar Malam Ibrahim Shekarau ne a hukumar zaɓe ta INEC.

Wannan na zuwa ne duk da irin ƙokarin da bangaren NNPP din suka yi na ankarar da INEC ɗin tare da rubuta musu takardar cewa sun sauya sunan Malam Shekarau da na Sanata Rufa’i Sani Hanga.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *