Alfijr ta rawaito Tsohon gwamnan Sokoto kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa ya nuna rashin dadinsa game da kalaman da gwamna Nasiru El Rufa’I ya yi, cewa babu sauran dattawa a arewacin kasar.

Bafarawa ya bayyana Kalaman da cin fuska ne kuma akwai rashin dacewa a ce El Rufai ya yi jam’i, saboda ai na kirki ba sa karewa.
Elrufa’I ya yi waɗannan kalamai ne a lokacin wata tattaunawa da BBC kan zargin da suke cewa akwai masu yi wa jam’iyyar zagon kasa, da ke fakewa da zance sauya takardun kuɗi domin ganin sun faɗi zaɓe.
Ya kuma ce, “Batun wani dattawa, ba wani dattawa, ni ma dattijo ne domin a wannan shekarar ta 2023 zan cika shekara 63, don haka su waye dattawan Arewan, mu gwamnonin Arewa mu ne dattawan Arewa kuma mune shugabannin Arewa.”
Attahiru ya ce ai shekaru, ba su ba ne dattako, domin akwai masu karancin shekaru amma kuma tunaninsa na manya ne da sanin ya kamata.
Ya kara da cewar karami mai hankali, nagartacce ya fi mai shekara 100, in dai batun na shekaru ne.
“Sannan da ya ke magana cewa shekarun sa 63, kuma baya ganin da sauran dattijai a arewa, to mu muna ganin waɗannan maganganu akwai rashin dattijantaka a cikinsu.
“Kalaman El-Rufa’i babu dattijantaka da girma a ciki, saboda abin da ya kamata ya yi shi ne, kalaman ci gaban arewa da ci gaban kasa da jama’a baki ɗaya.
“Sannan El-Rufa’i na maganar ya tsaya zaɓe an zaɓe shi, idan wannan shi ne dattijo to ai tun kafin ya yi takara mu muka yi kuma aka zaɓe mu”, in ji Bafarawa.
Abin da El-Rufa’i bai sani ba, shi ne arewa tafi karfin wani mutum guda, kuma duk mutumin da ya wulakanta ta ba zai gama lafiya ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Wannan Abinda Alh. Attashiru baffarawa yafada gaskiyane duk Wanda ya wulakanta AREWA Da MUTANENTA ya Allah danmatsayi manzon Allah (s.a.w.) Allah kawulakantashi Idan wata niima,wadata ko mulki taye/take takama dashi Allah karusashi danAlfarmar Annabi Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam
To a yanzu kenan,ya kamata El-Rufai ya bayyana sanda bakinsu ya taba haduwa a matsayinsu na dattawa (kamar yadda yanzu akan canjin kudi sukayi) don nemawa Arewa mufita akan matsalar tsaro,kunci da talauci daya shafi yankin.