
Alfijr ta rawaito Hukumomi a kasar Saudiyya sun kama mutane 138 da ke aiki a ma’aikatu daban-daban a wani mataki na yaki da cin hanci da rashawa.
Ana zargin mutanen da karbar cin hanci da rashawa, cin zarafi, karkatar da kudade da kuma jabu da dai sauransu.
Hukumar sa ido da yaki da cin hanci da rashawa ta Nazaha ta sanar a ranar Talata cewa ta binciki wasu mutane 308 da ake zargi da aikata laifuka da dama a cikin watan Safar 1444AH (Agusta-Satumba 2022).
Nazaha ta gudanar da zagaye na duba jimillar mutane 2,799.
Hukumar ta ce wadanda ake zargin sun hada da ma’aikatun tsaro, cikin gida, tsaro na kasa, lafiya, ilimi, kananan hukumomi da al’amuran karkara da gidaje, shari’a, sufuri da dabaru.
Sai dai daga bisani an bayar da belin wasu daga cikin wadanda ake zargin.
Nazaha ta yi kira ga jama’a da su ba ta hadin kai idan sun gano duk wani cin zarafi ko zargin cin hanci da rashawa na kudi ko gudanarwa ta hanyar bayar da rahoto ta lambar kyauta: 980 ko ta imel: 980@Nazaha.gov.sa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ