Badaƙalar N585m: EFCC ta titsiye Akanta-Janar tare da gayyatar ma’aikatan Ofishin Betta Edu

FB IMG 1704870772714

Hukumar EFCC ta titsiye Akanta-Janar ta Tarayya, AGF, Oluwatoyin Madein tare da kuma gayyatar karin ma’aikatan ma’aikatar jin kai kan zargin badakalar N585.2m.

Alfijir labarai ta rawaito wata majiya a EFCC ta bayyana cewa an gayyaci Misis Madein da wasu ma’aikatan ne bisa alaka da zargin da ake yi na N585.2m da ta shafi ministar jin kai da aka dakatar, Dr Betta Edu.

Majiyar ta ce jami’an EFCC sun yi wa AGF din tambayoyi na tsawon sa’o’i da dama a hedikwatar hukumar da ke Jabi, Abuja amma daga baya aka sake ta.

Majiyar ta ce an tambayi Misis Madein ne kan biyan Naira miliyan 585.2 na kudaden gwamnati daga ma’aikatar zuwa asusun ajiyar banki na wani jami’in gwamnati.

Madein, a cewar majiyar, ta shaida wa masu tambayoyin cewa ba ta sa hannu a kan takardar da ministar, Misis Edu ta aike mata na biyan kudin a wani asusu na ƙashin-kai ba.

“An yi mata tambayoyi ne na tsawon sa’o’i da dama a ranar Litinin kan biyan N585.2m daga asusun ajiyar kudi na National Social Investment Office (NSIO) zuwa asusun UBA na UBA na Bridget Oniyelu, Akanta na Tallafawa ga kungiyoyi masu rauni a karkashin ma’aikatar.

“Ta gaya wa masu binciken cewa ba ta saka hannu a takardar da Edu ta tura mata ba don biyan kuɗi a asusu na ƙashin-kai.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *