Alfijr ta rawaito Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, CBN, Godwin Emefiele, ya ce wa’adin ranar 31 ga watan Janairu na dakatar da karɓar tsoffin kudaden Naira ya na nan ba canji.
Emefiele ya bayyana hakan ne a yau Talata a Abuja, bayan taron kwamitin kula da harkokin kudi, MPC, na babban bankin.
A cewarsa, tazarar kwanaki 90 da CBN ta baiwa ‘yan Najeriya na mayar da tsofaffin kudadensu ya ishe su.

“Mun yi kira ga bankuna da su tsawaita lokacin aikinsu, kuma su yi aiki har a karshen mako.
“Babu dalilin yin magana game da canji. Sabbin kudaden suna nan,” in ji shi.
Mista Emefiele ya ce babban bankin ya umarc bankuna da su saka sabbin takardun kudi a cikin na’urorin bada kuɗi, wato ATM domin ƴan Nijeriya.
“Mun kara biyan su sabbin takardun kudi. Akwai isassun adadin sabbin kuɗaɗen.
“Mun yi imanin cewa ya zuwa ranar 31 ga watan Janairu, sabbin takardun naira za su mamaye lungu da sako na kasar nan,” in ji shi.
Emefiele ce zuwa yanzu CBN ya samu kusan Naira Tiriliyan 1.5 na tsofaffin takardun Naira.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su gaggauta daukar tsofaffin takardunsu zuwa bankuna kafin cikar wa’adin, ya kara da cewa kada su ji tsoron tsangwama ga jami’an tsaro.
“Mun roki EFCC da ICPC da su bar ‘yan Najeriya su ajiye tsoffin takardunsu na Naira,” inji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇