Jam’iyyar PDP Ta Gargadi Ganduje Kan Zuwa Rumfunan Zabe A Bayelsa

📸Umar Abdullahi Ganduje


Jam’iyyar PDP reshen jihar Bayelsa ta yi kakkausar suka kan ziyarar da shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, zai kai jihar kasa da sa’o’i 24 domin gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar din nan.

Alfijir Labarai ta rawaito Jam’iyyar PDP ta ce ziyarar za ta kara ta’azzara yanayin tsaro da ake fama da shi a jihar.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Sakataren yada labarai na PDP na jihar, Mista Ebiye Ogoli, ya ce jam’iyyar ta damu da yadda Ganduje ke shirin kai ziyara jihar a lokacin da INEC ta kayyade wa’adin yakin neman zaben jam’iyyun siyasa ya cika da tsakar daren ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwambar 2023.

Jam’iyyar PDP ta kuma bayyana cewa Shugaban jam’iyyar APC ba wani mai sa ido bane na kasa-da-kasa ko na cikin gida da aka amince da shi a zaben na ranar Asabar, kuma ba zai kada kuri’arsa a Bayelsa ba, kasancewarsa mai rijista a jihar Kano.

Sanarwar ta kara da cewa kasancewar Ganduje a Bayelsa zai tabbatar da zargin cewa jam’iyyar APC ta kammala shirin yin magudi a zaben da kuma bayar da cin hanci a tsakanin masu zabe da kuma alkalan zabe.

Bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, muna kira ga Shugaban jam’iyyar APC da ya fasa ziyarar da ya shirya kaiwa Bayelsa inji sanarwar.

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *