Babban Bankin Najeriya Ya Nemi Afuwar Ƴan Kasar


Alfijr ta rawaito Gwamnan babban bankin Najeriya CBN Mista Godwin Emiefele, ya nemi afuwar ƴan Najeriya bisa matsalolin da ake fuskanta yayin tura kuɗi ta Internet.

Godwin Emefiele, ya buƙaci hakan ne yayin taron kwamitin tsare-tsare kan harkokin kuɗi da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Haka kuma, ya tabbatar da cewa za a magance matsalar nan ba da jimawa ba.

Gwamnan na babban banki, ya ƙara da cewa, sashen da ke kula da biyan kuɗaɗe na babban bankin, na yin iyakacin kokarinsa wajen tabbatar da cewa an magance matsalar.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsaloli wajen aika kuɗi da wayoyinsu na hannu har ma a na’urar hada-hadar kuɗi ta POS.

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *