Babban Bankin Najeriya Ya Canja Shugabannin Bankunan Polaris, Union da Keystone.

IMG 20240111 105954

Babban bankin Najeriya CBN ya naɗa sabbin shugabannin wasu bankunan kasuwanci a Najeriya.

Alfijir labarai ta rawaito wata sanarwa da CBN ɗin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce bankunan da aka naɗa shugabannin sun haɗa da Polaris, Keystone da kuma Union.

Sanarwar ta CBN ta ce an naɗa Lawal Mudathir Omokayode Akintola, a matsayin shugaban bankin Polaris, sai Hassan Imam, wanda ya zama sabon shugaban bankin Keystone.

Sai kuma Yetunde Oni a matsayin shugabar bankin Union.

Naɗa sabbin shugabannin na zuwa ne bayan rusa kwamitocin gudanarwar bankunan da CBN ya yi saboda karya dokoki da suka yi, ciki har da shiga ayyukan da suke barazana ga harkokin kuɗi.

Matakin ba zato ba tsammani ya samo asali ne daga shawarwarin da mai bincike na musamman, Jim Obazee ya bayar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya nada a watan Yulin 2023 don yin nazari sosai kan ayyukan ba CBN kadai ba har ma da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi. Wannan yunkuri yana nuna wani muhimmin lokaci a cikin ci gaba da neman gaskiya da rikon amana a cikin fannin hada-hadar kudi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *