Atiku Da Obi sun yi martani kan rahoton BBC kan rashin samun hujjar zargin takardun Tinubu

FB IMG 1697127697278 edit 3959534304081

Tsagin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaran sa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, sun nuna rashin amincewarsu da rahoton BBC ta fitar na cewa babu wata shaida da ke tabbatar da zargin jabun takardun karatu da ake yiwa shugaba Bola Tinubu.

Alfijir Labarai ta rawaito BBC a wani rahoton binciken tantance gaskiyar labari da aka wallafa ranar Laraba ta ce babu wata shaida da ke nuna cewa Tinubu ya yi karya a takardar shaidar jami’ar Jihar Chicago da ya mika wa INEC.

Da yake mayar da martani, mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa ga Atiku Abubakar, Phrank Shaibu, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana rahoton na BBC a matsayin wani bangare na shirin farfaganda na gwamnatin Tinubu.

Su kuwa shugabancin jam’iyyar Labour ta bakin mai ba ta shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar, Kehinde Edun, ya ce rahoton da kafar yada labarai ta Burtaniya ta fitar bai girgiza su ba, wanda suka yi nuni da cewa yunkuri ne na kawar da labarin zargin da ake yiwa shugaban kasar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *