APC Za Ta Yi Taron Addu’a Don Neman Nasara A Kotu A Kano


Shugabannin jam’iyyar APC na Kano karkashin jagorancin Abdullahi Abbas sun umarci al’ummar Kano da ‘ya’yanta na mazabun 484 da ke Kano da su gudanar da tasu addu’a a ranar Litinin.

Alfijir Labarai ta rawaito shugabannin jam’iyyar APC a Kano sun kuduri aniyar gudanar da addu’o’i da azumi a ranar Litinin, sakamakon kalubalen da gwamnatin NNPP ta Kano ta gindaya, wanda ya shafi kasuwancin mutane, musamman ta hanyar rushe-rushe.

Shugaban jam’iyyar Abdullahi Abbas ya ce manufar addu’ar ita ce a roki Allah Madaukakin Sarki da ya kawo dauki da kuma daukaka darajar Kano.

Ƴaƴan jam’iyyar da dimbin magoya bayansu sun yi maraba da wannan umarni, suna dakon ranar da aka ware domin cika umarni.

Hakazalika shugaban jam’iyyar APC ya bukaci jama’a da su yi wa APC addu’ar samun nasara a kotun sauraren kararrakin zaben gwamna.

Nigerian Tracker

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *