Da misalin karfe 10 na safiyar Asabar 7/10/2023 , aka gabatar da sallar jana’izar mutum hudu wanda Mahara (kidnappers) suka kashe nan take a daren jiya juma’a, a Unguwan Dankali dake yankin Dan magaji a Zariya .
Alfijir Labarai ta rawaito yan ta’addan sun bayyana ne da misalin karfe 11 na dare , inda suka mamaye gidan Alh Musa ( Dan haki) basu sameshi shi ba, suka tafi da É—aya daga cikin matan shi , da sauran mata guda uku, sunyi ta barin wuta da bindigogi, sun harbi kusan mutum 9, inda mutum 4 suka rasu , mutum 5 kuma na Asibiti.
Dubban al umma ne suka halartarci jana’izar cikin alhini da da damuwa. limamin unguwar Malam Musa Tanko shine yajagoranci jana’izar.
Cikin taimakon Allah duka mata hudu da yan ta’adda suka dauka Allah ya kubutar dasu.
Muna rokon Allah ya jikan wanda suka rasu, ya baiwa masu rauni lafiya sannan yayi mana Maganin wannan musiba ameen


Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo