Alfijr ta rawaito wata amarya mai suna Khadija Abdullahi ta gamu iftila’in rasa idonta guda daya a hannun jami’an bijilanti a yankin shagalin bikinta a unguwar Kwajalawa a birnin Kano.
Lamarin ya faru ne a lokacin da amarya da kawayenta suke cashewa da kidan Dj , nan ne ake zargin wasu daga cikin jami’an bijilantin da far mu su da duka har amarya ta rasa idon nata.
A nasa bangaren angon Khadija Abdullahi wato Hamisu Bala ya bayyana cewa daman yan bijilantin sun yi ikirarin sai sun tarwatsa taron DJ din da ake yi.
Sannan ya yi kira ga mahukunta da bi masa kadi na illata masa amaryar tasa da bariinta da ido daya.
Mahaifin Amarya Mallam Abdu Ma’azu wanda ake kira Bako Dankasuwa ya bayyana takaicinsa da cewa yana Tudun Murtala aka kira shi a waya cewar an fasa idon yaraa, wanda da zuwansa ne ya sanarwa da jami’an yan sanda suka hadu tare suka kaita Asibiti.
Mahaifiyar amarya Haj Amina Abdu ta nuna damuwarta akan wannan al’amari ,wadda ta ce ranar farin ciki ta zame mu su ta bakin ciki .
Hakazalika Khadija Abdullahi wato Amarya ta zargi yan bijilantin da nuna mata bakin ciki karara a lokacin da take murnar bikin ta ,tare da kira ga mahukunta su kwato mata hakkinta.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇