Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta bukaci mata da su daina shiga masana’antar Kannywood, inda ta bayyana cewa illar shiga masana’antar da mata ke fuskanta ya fi alfanu dake cikin masana’antar.
Alfijir labarai ta rawaito Hadiza Gabon ta bayyana haka ne a wata hira da ta yi a shirinta na tattaunawa, wanda ake watsawa a tashar ta ta YouTube mai suna Gabon Show
Gabon ta yi wadannan kalamai ne ga bakuwarta, Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Surayya Aminu, wadda aka fi sani da Rayya, a lokacin da ta karbi bakuncin ta a cikin shirin.
Gabon ta shaida wa Surayya Aminu cewa, “Idan mace ta zo mini ta ce tana son shiga Kannywood, zan ba ta shawarar ta daina. Idan ta dage sai na yi mata fatan alheri. Amma ina gaya muku, ya fi kyau mace ta yi aiki tuƙuru, ta yi karatu, ta yi aure.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj