Ana Wata: Barkewar Gudawar Fasinja Tayi Sanadiyar Juyawar Jirgin Sama Yana Tsaka Da Tafiya Inda Ya Fito

Wani jirgin sama mallakin kamfanin sufuri na Delta da ke Amurka, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa birnin Barcelona daga Atlanta ya juya ala-tilas bayan da wani fasinja ya ɓarke da gudawa.

Alfijir Labarai ta rawaito tun farko dai jirgin ya kwashe awa biyu yana tafiya a sama, sa’ilin da matuƙin jirgin ya buƙaci sake juya akalar jirgin domin komawa inda ya taso.

A cikin wata murya da aka wallafa a shafin X, an ji matuƙin jirgin na cewa wani fasinja “ya feshe cikin jirgin da gudawa.”

A wata sanarwa da ya fitar, kamfanin sufurin jiragen sama na Delta ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an samu wata matsala wadda ta sanya jirgin ya koma Atlanta domin a tsaftace shi.

Sanarwar ta ce Jirgin Delta mai lamba 194 daga Atlanta zuwa Barcelona ya koma inda ya tashi bayan wani ya kamu da rashin lafiya lokacin da ake tsaka da tafiya.

“Ma’aikatanmu sun yi aiki cikin gaggawa inda suka tsaftace jirgin tas, sannan aka kai fasinjoji zuwa inda suka nufa.”

Kamfanin ya nemi afuwar fasinjoji kan jinkirin da aka samu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *