An Sake Gurfanar Da Jaruma Hadiza Gabon Gaban Kotun Shari’ar Musulunci

Alfijr ta rawaito a ranar Juma’a ne Kotun Shari’a da ke zamanta a Magajin Gari Kaduna ta mika karar da aka shigar da fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Hadiza Aliyu-Gabon zuwa Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jihar Kaduna.

Alkalin kotun, Isiyaku Abdulrahman, ya mika karar zuwa babbar kotun shari’a da ke Tudun Wada, biyo bayan rokon lauyan mai kara, Nurudeen Murtala.

Yayin mika karar, alkalin ya zargi lauyan da son bata lokacin kotun.

Ya kara da cewa “Kuna da zaɓuɓɓuka biyu.

Daya shi ne in soke karar ko kuma in mika ta zuwa wata kotu,” in ji alkalin.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa Bala Musa wani ma’aikacin gwamnati ne ya maka jarumar kotu saboda ta ki aurensa.

Mista Musa ya shaida wa kotun cewa, “Ya zuwa yanzu na kashe mata N396,000.

Duk lokacin da ta nemi kudi nakan ba ta ba tare da wata damuwa ba tare da fatan za mu yi aure”.

Wadda ake karar wadda ta yi magana ta bakin lauyanta, Bar. Mubarak Sani ya musanta sanin Mista Musa yana mai cewa ba ta taba ganinsa ko haduwa da shi ba, kuma ba ta da wata alaka da shi.

hdrpl

Lauyan wanda ya shigar da karar ya gabatar da kwafin takardar banki ga kotun kuma ya shaida wa kotun cewa wasu mutane hudu ne suka karbi kudin da aka ce an aika wa wanda ake kara Hadiza Gabon.

Biyu daga cikin hudun, Fatima Abdullahi da Abdullahi Yusuf sun yi ikirarin cewa aminin wanda ake kara ne kuma mataimaki na kan su.

Sun amsa laifinsu na yin kwaikwayon jarumar tare da karbar kudi da Sunanta, suna rokon kotu ta gafarta musu.

A takaice dai bayan kammala shari’ar, lauyan ‘yar wasan ya shaida wa manema labarai cewa suna bukatar kotu ta sallami wanda ya ke karewa saboda ba ta yi zamba ba ko kuma ta sabawa wani amana kamar yadda ake tuhuma a baya.

Lauyan wanda ya shigar da karar a daya bangaren ya ce adalci ne kawai ya ke so

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

One Reply to “An Sake Gurfanar Da Jaruma Hadiza Gabon Gaban Kotun Shari’ar Musulunci”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *