Dakarun Rundunar Sojin Najeriya sun ceto ƙarin mutane hudu da yan bindiga su ka sace, yayin da ake ci gaba da farmakin da ake kai wa fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Kachalla Muhammadu Fulani, da mabiyansa a Jihar Katsina.
Kwamishinan Harkokin Tsaro na Cikin Gida na Jihar Katsina, Dakta Nasir Mu’azu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar Laraba.
A cewar sanarwar, mutanen da aka ceto sun kasance tare da marigayi tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya (DDI), Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasu a hannun masu garkuwa da mutanen a karshen makon da ya gabata. Tun da farko dai dakarun soji sun samu nasarar ceto matarsa, Hajiya Amina Rabe Abubakar.
Gwamnatin jihar ta bayyana sunayen wadanda aka ceto da suka hada da Musa Yakuba mai shekaru 62, Alhaji Sa’adu Dayi mai shekaru 68, Mukhtar Danja mai shekaru 36, da Salisu Danja mai shekaru 50.
Sanarwar ta ce an ceto su ne sakamakon ci gaba da hare-haren soji a wuraren da ake zargin ‘yan bindigar suna buya.
Bayan ceton nasu, jami’an lafiya sun ba su kulawar gaggawa saboda raunukan harbin bindiga da suka samu yayin da suke tsare a hannun masu garkuwar.
Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda ta yabawa jajircewa, kwarewa da sadaukarwar dakarun soji da sauran jami’an tsaro da suka gudanar da aikin.
Ta kuma tabbatar wa al’umma cewa jami’an tsaro na ci gaba da bibiyar Kachalla Muhammadu Fulani da sauran masu aikata laifuka domin kamo su tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Gwamnatin ta jaddada aniyarta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da cewa babu wani wuri da masu laifi za su samu mafaka a fadin jihar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t