An Saka Ranar Fara Ɗiban Alhazan Najeriya Zuwa Saudiyya

Alfijr ta rawaito Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta ce za ta fara aikin jigilar maniyyata hajjin bana zuwa ƙasa mai tsarki daga ranar Alhamis 25 ga watan Mayu.

Kwamishinan harkokin ma’aikata da kuɗi a hukumar, Nura Hassan Yakasai, ya shaida wa BBC cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen wajen fara jigilar mahajjatan bana, inda ya ce alhazan jihar Nasarawa za a fara ɗiba a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

Ya ce za a kuma kammala kwashe alhazan Najeriya a ranar 18 ga watan Yuni.

Nura Yakasai ya yi kira ga maniyyata da cewa duk wanda aka kira ya tabbata ya fito a kan lokaci domin fara aikin ba tare da samun tsaiko ba.

A ranar Asabar ne alhazan farko daga ƙasashen Malaysia da Bangladesh suka isa Saudiyya domin fara aikin hajjin bana.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *