An Rushe Gini 5,000 Da Aka Yi A Ƙarƙashin Manyan Layukan Lantarki A Najeriya

Alfijr ta rawaito shugaban hukumar kula da harkokin wutar lantarki a Najeriya ta, wato Nigerian Electricity Management Service Agency (NEMSA) ya ce sun rusa gine-gine kusan 5,000 da ke ƙarƙashin manyan wayoyin lantarki a faɗin ƙasar.

Aliyu Tahir wanda shi ne kuma babban jami’in lantarki na ƙasa, ya faɗa a yau Juma’a cewa tun 2017 aka ɗauki mataki tare da ba da umarnin rushe gine-ginen da ke ƙarƙashin wayoyin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.

NEMSA ta ce akwai buƙatar gaggauta katse yankunan daga layin lantarki da kuma rushe su daga baya.

“A ɓangarenmu, mun bai wa kamfanonin rarraba lantarki umarnin sauke duk wani gini da aka yi a ƙarƙashin babban layin lantarki daga kan layin wutar, har ma da waɗanda suka tare hanya,” a cewarsa.

Tahir ya ƙara da cewa rushe gine-ginen na buƙatar himma daga waɗanda abin ya shafa, “kamar gwamnatin tarayya da ta jihohi”.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *