Gwamnatin jihar Kano ta rufe asibitoci 12 da kuma soke lasisin wasu asibitoci masu zaman kansu 3 saboda cin zarafi daban-daban a watannin baya.
Alfijir labarai ta ruwaito babban daraktan hukumar kula da cibiyoyi lafiya masu zaman kansu na jihar Kano PHIMA Farfesa Salisu Ahmed Muhammad ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta musamman da gidan rediyon Najeriya a Kano.
A cewarsa, asibitin fadar, lafiya tafi kudi da ma’aikatan lafiya na Minjirya gaba daya an soke su daga aikinsu a jihar, yayin da wasu 12 kuma aka rufe su har sai an kammala tantance su.
Ya ci gaba da cewa, PHIMA ta tsara taswirar likitocin gargajiya sama da 4,000 a jihar kuma za ta ba su lasisin yin aiki.
Shugaban hukumar ya yi nuni da cewa, hukumar ta kuma hada cibiyoyin koyar da kiwon lafiya da makarantu domin horas da su a hukumance da shigar da su cikin ayyukan kiwon lafiya.
Farfesa Salisu ya yi nuni da cewa gwamnati mai ci ta samar wa PHIMA ofishin dindindin, domin tana gudanar da aiki a wani gidan haya tare da sanya matattarar hasken rana don tabbatar da samar da wutar lantarki akai-akai, da fitar da kudaden da ake kashewa a kan kari da kuma samar da ababen hawa.
Ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarori da dama da suka hada da “Bitar dokar hukumar ta 2017, ka’idojin kyamist da sauran shagunan magunguna, tsarin dabarun shekaru 5, yarjejeniyar na ma’aikata da sauransu”
Shugaban ya kara da cewa hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu PHIMA ta ba da umarnin yin rijistar asibitoci, dakunan shan magani, dakunan gwaje-gwaje, dana motsa jiki, cibiyoyin jinya, likitocin gargajiya da dai sauransu.
Farfesa Salisu ya ce ana sa ran dukkanin cibiyoyi da ke karkashin PHIMA za su sabunta rijistar su duk shekara, yana mai cewa hukumar ta sanya takunkumi ga duk wanda ya ki bin umarnin.
Ya yabawa gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da kwamishinan lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf bisa namijin kokarin da suke yi na ganin an samar da ingantaccen kiwon lafiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj