
Alfijr ta rawaito rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori ‘yan sanda 18 bisa laifuka daban-daban da suka hada da cin zarafi da rashin da’a da kuma karbar cin hanci da rashawa.
Idan za a tuna a ranar 4 ga watan Oktobar shekarar 2022, hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kori wasu manyan jami’an ‘yan sanda bakwai bisa zargin aikata rashin da’a tare da amincewa da ragewa wasu jami’ai 10 karin girma.
Hukumar ta PSC ta ce jami’an da aka kora sun hada da babban Sufuritandan ‘yan sanda, Sufuritanda na ‘yan sanda daya, da mataimakan Sufiritandan ‘yan sanda biyar, Ya kara da cewa SP daya ya yi ritaya ne domin amfanin jama’a.
Hukumar ta kuma rage darajar CSP zuwa SP, SP uku zuwa DSP; DSP guda biyu zuwa ASPs, da ASP hudu zuwa Insifakta.
A ranar 22 ga watan Disambar shekarar 2022, kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, Muhammed Berde, ya bayyana cewa rundunarsa ta kori ‘yan sanda bakwai bisa samun su da cin mutuncin aikin ‘yan sanda.
Hukumar NPF a ranar 13 ga watan Afrilu, 2023, ta kori wasu manyan ‘yan sanda 3, bisa laifin amfani da makami, cin zarafi, rashin da’a da kuma almubazzaranci da harsasai.
Wadanda lamarin ya faru gare su sun hada da, Insifekta Dahiru Shuaibu da Sajan Abdullahi Badamasi da Isah Danladi – wadanda ke tare da wani mawakin Kano ne a yayin da masu rakiyar aka dauki hoton bidiyo suna harbin iska.
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta a ranar 19 ga watan Afrilu, 2023, ta kori Insifekta Ubi Ebri bisa zargin kashe wani matashi dan shekara 26, Onyeka Ibe, a hanyar Ugbolu-Illah a garin Asaba bisa zarginsa da kin bayar da cin hancin N100.
A halin da ake ciki kuma, wani lauya mai kare hakkin bil’adama mazaunin Abuja, Pelumi Olajengbesi, ya yabawa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, kan yadda ya kiyaye da’a a rundunar.
Olajengbesi, wanda shi ne Manajan Abokan Hulɗa a Law Corridor, ya ce idan aka ci gaba da ɗorawa da kuzari da ƙima na ƙwararru da tsattsauran matakan ladabtarwa, ‘yan sanda za su ga gagarumin sauyi wanda zai rage yawan kashe-kashen da ‘yan sanda ke yi ba tare da shari’a ba.
Ya kara da cewa, “IGP Usman Alkali Baba a ‘yan kwanakin nan ya fito karara ya nuna hazakar shugabanci da sanin ya kamata ta hanyar tabbatar da an gurfanar da jami’an da suka aikata laifi ba bisa ka’ida ba.
“Mun shaida yadda ake korar jami’an da suka aikata miyagun laifuka da, rage musu girma da kuma gurfanar da su gaban kuliya, tun daga karbar kudade da zalunci da kashe-kashe ba gaira ba dalili.
The Punch
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ