Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa an kama wasu ‘yan sanda da ke ba shahararren mawakin nan na Kano Dauda Kahutu Rarara kariya.

Hakan na zuwa ne yayin da wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga ‘yan sandan da ke ba mawakin kariya suna bin sa a baya har ya shiga mota bayan haka suka soma harba bindiga a sama.
Sai dai a wani sako da mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya Muyiwa Adejobi ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce rundunar ‘yan sandan kasar ta yi tir da “rashin kwarewa da kuma halaye na rashin ɗa’a da ‘yan sandan suka nuna, inda suke harba bindiga domin kambama mawakin na Kano.
Hukumar ta ce an gano ‘yan sandan kuma an kama su.
Za a kai su hedikwatar ‘yan sanda domin yi musu tambayoyi da kuma daukar matakan da suka dace,” kamar yadda ya kara da cewa.
Haka kuma ya ce irin wannan ɗabi’a ba ta ‘yan sanda ba ce kuma
ba za su lamunci hakan ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ
Very good news