
Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sandan ta kama wata malama bisa zargin yi wa wani yaro ɗan shekara 4 fyade a jihar Borno.
Malamar mai suna Aunty Zara da ke aiki da makarantar Golden Olive da ke Maiduguri babban birnin jihar, an ce ‘yan sanda sun kama ta a makon jiya.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, Sani Kamilu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ya ce mahaifin yaron ne ya kai karar ga ‘yan sanda, inda ya kara da cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin.
Hassan Dala, mahaifin ya lura fitsarin ɗan nasa ja ne. “Da farko, na ɗauka alama ce ta kamuwa da cuta, sai na kai ta asibiti, suka gaya mana mene ne matsalar,” in ji Dala.
“Lokacin da mahaifiyar ta tambaye yaron, sai ya gaya mana abin da malamar ta yi masa.
Yaron ya ce malamar ta rungume shi, ta ba nononta ya tsotse, sannan ta sanya yatsa a cikin al’aurar ta.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ