An Kama Wanda Ake Zargi Da Kashe Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda A Katsina

Ƴan Sanda A Katsina Sun Kama Waɗanda Ake Zargi Da Kashe Kwamishinan Ƴan Sanda a Katsina yayin musayar wuta.

Alfijir Labarai ta rawaito rundunar yan sanda a jihar Katsina sun kama wani Sa’idu Yaro da ake zargi da hannu cikin waɗanda su ka hallaka mataimakin kwamishinan yan sanda.

An hallaka Aminu Umar da wani jami’in ɗan sanda kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Haka na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar.

Ana zargin Sa’idu Yaro wanda ya daɗe ana nema ruwa a jallo da haɗa kai da aikata muggan laifuka a jihar.

Daga cikin laifin da ake zarginsa da aikatawa har da kisan babban jami’in ɗan sanda a jihar.

A cikin sanarwar da ke nuna ayyukan rundunar da nasarorin da ta samu, kakakin ƴan sandan ASP Abubakar Sadiq ya ce sun samu nasarar kama mai kaiwa yan bindiga bayanai, da kuma kwato harsashi mai yawa daga wajensa.

Haka kuma akwai wani Saminu Usman mai shekaru 19 a duniya, wanda aka kama ana zarginsa da yin garkuwa da wani yaro mai shekaru biyar a duniya.

Rundunar ta ce su na ci gaba da bincike a kan mutanen da ake zargi, yayin da wasu tuni su ka amsa laifunsu.

Matashiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *