An kama mutane 9 da zargin amfani da audugar mata da famfas wajen haɗa matashin-kai

IMG 20231229 110723

Hukumar tsaron farin kaya ta kasa, NSCDC, ta kama wasu mutane tara da suke haɗa wa da siyar da matashin kai da suke cika shi da famfas din yara da audugar mata da akayi anfani da su a Sakwkwato.

Alfijir labarai ta rawaito da ya ke gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar a jiya Laraba, kwamandan jihar, Bello Alkali Argungun, ya ce kamasu ya biyo bayan rahoton sirri da su ka samu.

Ya ce, “Sun yi amfani da yara kanana da suke kawo musu shara. Sun cika kwandon matashin kai da shi wanda suke sayar wa kwastomominsu. Kayan matashin kan na ɗauke da tambari daban-daban na sanannun kamfanonin yin katifa.”

A cewar Argungun, hakan na iya yin illa ga lafiyar masu amfani da matashin kan.

“Suna iya kamuwa da wasu cututtuka ba tare da sanin musabbabin hakan ba. Ina kira ga jama’armu da su rika zuwa kasuwa da suka dace domin sayen kayayyaki,” inji shi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *