An Gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya Da Ya Gurfana Gaban Kotun Sauraron Kararrakin Zabe

FB IMG 1713862800982

Daga Aminu Bala Madobi

Kotun ta bukaci halartar Gwamnan babban bankin ƙasa CBN domin bayar da ƙarin haske kan yadda babban bankin ya shiga Zaɓen jihar da aka Gudanar a Ranar 11 ga watan Nuwamba 2023.

Alfijir Labarai ta rawaito bayan da Alex Izinyon (SAN) da ke zaman lauyan Gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo, ya shigar da kara a Ranar Litinin, an gayyaci Cardoso. Gwamnan da yake zama na biyu a cikin karar da jam’iyyar Social Democratic Party SDP da dan takararta, Muritala Ajaka suka Gabatar, ana bukatar ya mayar da martani.

Bayan da Gwamnan babban bankin CBN ko wani jami’in bankin ya gaza bin sammacin kotun da aka bayar a Ranar 18 ga Afrilu, Izinyon ya yanke shawarar mika takardar.

Ya bayyana cewa hukumar ta CBN ta bayyana a wata wasika da ta aike wa kotun cewa ba za su samu halarta ba har sai ranar Juma’a 26 ga watan Afrilu Saboda neman sammacin da suka yi.

Ya kara da cewa duk da cewa Ododo ya shirya Gabatar da shaidunsa cikin kwanaki biyar, Amma ya zama wajibi a saurari sammacin kafin Gwamnan ya ci gaba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *