An Dakatar da Muhyi Magaji Daga Shugabancin Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta jihar Kano

FB IMG 1712238970919

Kotun Da’ar ma’aikata ta dakatar da Muhyi Magaji daga shugabancin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano

Alfijir labarai ta rawaito Kotun da’ar ma’aikata ta dakatar Muhuyi Magaji daga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka gurfanar da Magaji a gaban kuliya bisa manyan zarge-zarge, da suka hada da saba ka’idojin da’a ga jami’an gwamnati, da yin rikici da juna, cin zarafin ofishinsa, da bayar da bayanan karya kan bayyana kadarorinsa.

Ana kuma zarginsa da cin hanci da karbar kyaututtuka.

Kotun ta goyi bayan wanda ya shigar da karar, inda ta umurci Magaji da ya ajiye mukaminsa na Shugaban Hukumar.

Ba zai iya cika aikinsa a Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ba har sai an saurari tuhume-tuhumen da ake yi masa, sannan a yanke hukunci.

Bugu da kari, kotun ta umurci gwamnan jihar Kano da sakataren gwamnatin jihar da su nada shugaban riko na hukumar domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan hukumar a wannan lokaci.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *