Shugabar Kotun Daukaka Kara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta mika dukkan kararrakin zabe da ke gaban kotun a jihohi 36 zuwa rassan kotun dauka Kara dake Abuja da Legas.
Alfijir Labarai ta rawaito cewar duk wasu kararrakin da aka daukaka na daga hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe daban-daban na jihohi 36 na kasar za a saurare su kuma za a tantance su a rassan kotun dake Abuja da Legas.
Bisa ga wannan mataki na Dongban-Mensem, cikin rassan kotun dauka Kara guda 20 da ake da su a kasar, guda biyu kadai cikin kotun za su saurari duk wasu kararrakin da suka taso bayan hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe a duk fadin kasar.
Umurnin ya shafi zabukan gwamnoni, na yan majalisun kasa da na jihohi.
Mensem ta yi hakan ne a matsayin mayar da martani ga dimbin koke-koke da zanga-zangar da wasu jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu suka yi, inda suka yi zargin cewa gwamnonin jihohi sun kawo cikas ga alkalan kotunan yayin shari’ar a tarabunal.
Rahotanni sun nuna cewa mai shari’a ta kaddamar da bincike mai zurfi kan zargin da ake wa gwamnoni da alkalan kotun sauraron kararrakin zabe.
Binciken da aka yi ya tabbatar da gaskiyar zarge-zargen kulla alaka tsakanin wasu gwamnoni da alkalan kotuna, wanda ya kai ga gurbata hukuncin Shari’un da kotun suka yanke.
Rahotanni sun bayyana cewa an gurfanar da wasu alkalan kotunan kotun, kuma suna iya fuskantar tuhuma daga hukumar kula da harkokin shari’a ta kasa (NJC).
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo