An Baiwa Hammata Iska a Babban taron APC na Arewa Maso Gabas a Gombe

IMG 171929 15625 1750004386333

Daga Aminu Bala Madobi

Hayaniya ta barke a babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Gabas da aka gudanar a babban Dakin Taro na Ƙasa-da-Ƙasa da ke Gombe.

Rigimar ta samo asali ne daga rashin furta kalaman “Sai Tinubu, Sai Kashim” a 2027, kalaman da suka zama dalilin shirya taron.

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa daga yankin Arewa maso Gabas, Kwamared Mustapha Salihu, ya jawo cece-kuce lokacin da yake gabatar da jawabi ba tare da ya bayyana cikakken goyon bayan sa ga mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ba.

Wannan rashin furta kalaman ya haifar da doke-doke da hayaniya, inda mahalarta taron suka fara ihu da hayaniya na tsawon mintuna goma.

Bayan matsin lamba daga shugabannin, Mustapha Salihu ya koma kan munbari ya furta kalaman “Sai Tinubu, Sai Kashim,” amma sai da aka ɗauki lokaci kafin ya samu damar ci gaba da jawabin.

A yayin da hayaniya ke tsananta, fiye da rabin mahalarta taron sun watse daga dakin saboda tsoron barkewar rikici.

Duk da haka, sauran shugabanni sun cigaba da gabatar da jawaban su, amma mafi yawansu ba su ambaci sunan Kashim Shettima ba.

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi nasa jawabin inda ya ce an basu kuri’u miliyan ɗaya da dubu dari biyu a zaben 2025. Sai dai, ya nemi goyon bayan jama’a don ƙarin nasara a zaben gaba, amma bai ambaci sunan Kashim Shettima kai tsaye ba.

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana goyon bayansa ga zarcewar Tinubu tare da Kashim Shettima. Amma Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, Da Gwamna Inuwa Yahaya Na jihar Gombe suma basu bayyana wannan goyon bayan kai tsaye a cikin jawabin nasa ba.

Rikicin ya janyo aka tashi daga taron ba tare da an kammala muhimman ajandodin taron ba.

Wannan ya sanya taron ya kare da matsala, yayin da masu ruwa da tsaki suka bar taron cikin rashin gamsuwa.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *