
Alfijr ta rawaito babban Limamin Harami Sheikh Sudais ya kaddamar da wata na’ura wadda za ta taimaka wajen hana yara bacewa a masallatai masu daraja Ka’aba da na Annabi a ranar Laraba.
An samar da Na’urar ne don samar da wata takardar shaida da za a rinka makalawa a hannun kanana yara a duk lokacin da za su shiga daya daga cikin masallatan.
An kuma bayyana cewar za a rubuta sunan yaro da kuma lambar wayar iyayensa a kan takardar, wanda hakan zai bayar da damar kiran iyayen yaro da zarar ya bace ko wani akasin.

Bayanai sun nuna yara da dama na bacewa a cikin jama’a a masallatan Ka’aba da na Annabi saboda yawan mutanen da ke ziyartar masallatan domin ibada.
📸 – Haramain Sharifain
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ