Shugaban riko na kungiyar yanjarida mawallafa Labarai ta yanar gizo Abdullateef Abubakar Jos ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayi Abdullahi Yakubu, wakilin jaridar Leadership na jihar Kano, wanda ya rasu a ranar Juma’a, 18 ga watan Agusta, 2023.
Kungiyar ta kuma jajantawa alummar jihar Kano da kungiyar Yanjarida ta kasa reshen Jihar Kano , da Correspondents Chapel na Kano.
A wata sanarwar manema labarai da shugaban riko, Abdullateef Abubakar Jos, wanda kuma mawallafin jaridar SOLACEBASE ya raba wa manema labarai, ya ce rasuwar Abdullahi Yakubu babbar asara ce ga aikin jarida a Kano da ma Najeriya baki daya, duba da irin gudunmawar da ya bayar, don bunkasa sana’a.
Sanarwar ta kara da cewa ‘Kungiyar Yanjaridar Mawallafa Labarai ta Intanet Dake Kano da shugabanninta sun samu labarin rasuwar babban abokin aikinsu cikin matukar kaduwa, tare da bayyana cewa Abdullahi Yakubu ya shahara da hakuri da jajircewarsa ga wannan sana’a tun zamanin da ya yi aiki da kamfanin buga jaridu ns Triumph
Kungiyar mawallafan sun yi addu’ar Allah Ta’ala ya baiwa iyalansa karfin gwuiwar jure rashinsa
Kamar yadda Abdullateef Abubakar Jos Shugaban riko da Abbas Yushau Yusuf Sakataren riko suka sawa hannu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM