Alhasan Ado Doguwa Na Zawarcin Kurejar Shugabancin Majalisar Wakilai

Alfijr ta rawaito Shugaban Masu rinjaye a zauren majalisar Wakilai Alhasan Ado Doguwa ya bi sahun masu zawarcin neman shugabancin zauren majalisar wakilan kasar nan.

A wata wasika  ta baiyana kudirinsa  da  Alhasan Ado Doguwa  ya aike da ita  ga zababbun  ‘yan Majalisar  Wakialan,  Ya baiyana cewar  aniyarsa  ta neman matsayin ya biyo  bayan  kishin da yake dashi  na  gina  cigaban kasa.

A yanzu haka  dai  sakamakon bayyana  aniyarsa  ta neman kakakin zauren majalisar  wakilai  da  ya  yi,  yawan masu neman  matsayin yanzu haka sun kai  11.

Bayyana burin nasa na zuwa  ‘yan kwanaki, Bayan da wata babban kotun jihar  Kano ta umarci  babban lauyan gwamnatin jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan ya shigar da tuhumar  zargin da ake  yiwa  Doguwa  da hannu wajen aikata kisan kai da kuma kona wasu kadarori  a  yayin  zaben shugaban kasa  dana  ‘yan Majalisar  dokokin taraiyya da aka yi a kwanakin baya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *