Babbar Akanta Janar ta Najeriya, Dakta Oluwatoyin Madein, ta ce ba ofishinta ne ke biyan kuɗin ayyuka ko wasu shirye-shirye da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin suka aiwatar ba.
Alfijir labarai ta rawaito Dakta Madien na martani ne kan rahotonnin wasu kafofin yaɗa labarai game da wata buƙata daga ma’aikatar jin-ƙai da yaƙi da fatara ta ƙasar, ta biyan kuɗin tallafi ga wasu masu ƙaramin ƙarfi a wasu jihohin ƙasar.
Ta ce ana ware wa kowace ma’aikata da hukuma kudaɗenta a asusun hukumarsu, kamar yadda ƙunshe cikin kasafin kuɗin ƙasar, kuma kowace ma’aikata ita ce ke ce da alhakin gudanar da ayyukansu da biyan kuɗin ayyukan da ta aiwatar.
Cikin wata nasarwa da ofishin babbar akantan ya fitar, ta ce duk da ofishinta ya karɓi takardar buƙatar biyan kuɗaɗen daga ma’aikatar jin-ƙayi da yaƙi da fatara ta ƙasar, amma ofishinta bai biya kuɗaɗen ba.
Ta ƙara da cewa ofishin nata ya shawarci ma’aikatar kan matakan da za ta bi wajen biyan kuɗaɗen kamar yadda dokar biyan kuɗaɗe ta tanadar.
Babbar Akantan ta kuma ce a irin wanna yanayi, ma’aikatun da abin ya shafa ne ke biyan kuɗaɗen zuwa asusun mutanen, ba tura maƙudan kuɗaɗe zuwa asusun wani mutum da sunan kuɗin gudanar ayyuka ba.
Ta ƙara da cewa a irin wannan biyan kuɗi ya kamata a tura kuɗin zuwa asusun mutanen da ake bai wa tallafin.
Daga ƙarshe sanarwar ta sake jaddada aniyar Dakta Made na yin aiki bisa doka ba tare da rufa-rufa ba wajen gudanar da kuɗaɗen gwamnati.
Ta kuma shawarci ma’aikatu da hukumomin gwamnati da koyaushe su tabbatar da sun bi doka da oda wajen gudanar da harkokin kuɗaɗe.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl