Aika Aika! Ya Kashe Jami’in Kotu Kan Kawo Masa Takardar Sammaci

ALFIJIR 1

Wani mutum da aka kaiwa takardar sammaci ya soka wa ma’aikacin kotun wuka ya kashe shi.

Alfijir labarai ta rawaito Mutumin ya yi wa akawun kotun wannan aika-aika ne a unguwar Kugama Wuro Jibir, Karamar Hukumar Mayo Belwa da ke Jihar Adamawa.

Ma’aikacin kotun mai suna Yauba Usman ya kai masa takardar sammaci ne daga kotun yanki na Nasarao Jereng, amma mutumin ya ki karba.

A maimakon haka, sai mutumin ya zaro wuka ya rika soka wa ma’aikacin kotun, ya ji masa raunuka, lamarin da ya sa aka kai shi asibiti, amma rai ya yi halinsa.

Kakakin ’yan sandan jihar Adamawa, SP Sulaiman Nguroje ya ce a sakamakon haka runduarsu ta cafke wanda ya yi wannan aika-aika, ana masa tambayoyi a ofishinsu.

SP Nguroje ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Afolabi Babata ya ba da umarni a zurfara bincike a kan lamarin.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *