
Alfijr ta rawaito ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC, ta umarci ma’aikata da su tsunduma yajin aiki daga ranar Larabar 29 ga wannan watan da muke ciki na Maris.
Shugaban ƙungiyar Joe Ajaero, ne bada ya da umarnin yau Laraba.

Haka kuma ya ce, gamayyar kungiyoyin da suka kafa kungiyar kwadagon ta Najeriya za su kasance cikin shiri domin yin zanga-zanga a dukkan sassan babban bankin CBN.
Umarnin dai ya biyo bayan ƙarewar wa’adin da NLC ɗin ta bai wa gwamnatin tarayya a makon jiya bayan da ta soki manufofin gwamnatin tarayyar na sauya tsofaffin kuɗi da sababbi.

Shugaban na NLC, ya ƙara da cewa duk da hukuncin da kotun koli na ci gaba da amfani da tsofaffin takardun Naira 500 da Naira 1000 har zuwa ranar 31 ga watan Disamban bana amma lamarin bai sauya zani ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
gwamnati Nigeria tazama abinda ta zama